An ci mutunci cutar Korona a jihar Bauchi akan ilimi

HomeFeaturedUncategorized

An ci mutunci cutar Korona a jihar Bauchi akan ilimi

Gwamnatin jihar Bauchi ta ce za a bude makarantun sakandire da firamare  a jahar domin cigaba da gudanar da karatu daga 12 ga watan Oktoba na shekara

Dan majalisar tarayya Eng Abubakar zai dauki nauyin karatun daliban kimiyya 100 har zuwa jami’a
Za a bude gidan Rediyo da Tv irin su na farko a Kano
Kawu Sumaila ya nemi a hukunta Adam Oshieomole

Gwamnatin jihar Bauchi ta ce za a bude makarantun sakandire da firamare  a jahar domin cigaba da gudanar da karatu daga 12 ga watan Oktoba na shekara ta 2020.

Kwamishinan ilimin jihar Dr. Aliyu Tilde, shi ne ya shedawa manema labarai hakan a Juma’ar nan  a harabar ma’aikatar, in da ya ce tun a watan Maris cikin karshen  zangon  karatu na karshe aka garkame makarantun saboda cutar korona.

Idan za a iya tunawa tuni jihohin Lagos, Oyo, Kogi, Taraba su ka bude makarantunsu tare da cigaba da karatu sakamakon raguwar yaduwar cutar korona/

COMMENTS

WORDPRESS: 0
error: Alert: Content is protected !!