Jam'iyar APC a karamar hukumar bichi da ke jihar Kano a Arewa Najeriya, ta tsayar da Farfesa Yusuf Muhammad Sabo, a matsayin dan takarar shugabancin k
Jam’iyar APC a karamar hukumar bichi da ke jihar Kano a Arewa Najeriya, ta tsayar da Farfesa Yusuf Muhammad Sabo, a matsayin dan takarar shugabancin karamar hukumar Bichi a zaben da ke tafe, farfesan wanda ya ke kwararran likita kuma malami a jami’ar Bayero da ke Kano, ya samu nasarar zama dan takarar ne biyo bayan amincewar masu zabe duba da kwarewa da cancantarsa.
Yanzu haka, tuni al’ummar karamar hukumar Bichi, sun dauki sowa da murna tare da bayyana amincewarsu da zabin farfesa Sabo, domin a cewarsu yana da tsare tsaren ciyar da karamar hukumar Bichi gaba, duba da irin gudunmuwar da ya bayar lokacin da ya rike kantoma.
Da ya ke jawabi a wata ziyarar da ya kawo BRTV wato Bichi Radio da Tv, dan majalisar jaha mai wakiltar Bich, Hon Lawan Shehu, ya bayyana zaben Farfesa da cewa masu zaben sun yi abin da yakamata, saboda kwarewarsa da zurfin ilimi, in da ya ce yana da tsare tsaren ciyar da karamar hukumar gaba.
Tsayar da Farfesa Sabo, masana na ganin cewa an daga kimar jihar Kano da Arewacin Najeriya.
COMMENTS