An yi bikin kaddamar da jaridar Wafiya karo na uku

HomeLabarin Wasanni

An yi bikin kaddamar da jaridar Wafiya karo na uku

A yau ne aka sake gudanar da bikin kaddamar da jaridar Wafiya karo na uku, wanda sanannan mai gabatar da shirin wasannin nan Wasilu Kawo, na gidan red

Why mom was right about operating systems
How amazing gadgets are making the world a better place
18 podcasts about cool science experiments

A yau ne aka sake gudanar da bikin kaddamar da jaridar Wafiya karo na uku, wanda sanannan mai gabatar da shirin wasannin nan Wasilu Kawo, na gidan rediyon Raypower ya ke rubutawa, taron wanda aka gudanar a yau Juma’a a harabar makarantar firamare da ke Kawon mai gari, a karamar hukumar Nasarawaa jihar Kano, ya samu halartar manyan baki magoyabayan kungiyar kwallon kafa musamman magoyabayan kungiyar Barcelona da Real madrid ds.

Yayin taron an buga wasan karshe na sada zumunci tsakanin kungiyar  kwallon kafa ta Kawo Warrious a matsayin mai masaukin baki, da takwarar ta A,D.S Zaura, inda aka ta shi A.D.S ta jefa kwallaye biyu a ragar Kawo Warrious ta hannnun ‘yan wasa Abdullahi da Messi.

Bayan tafiya hutun rabin lokaci, shugaban magoya bayan Barcelona Alhaji Bala Abi doka, ya jagoranci kaddamar da jaridar Wafiya tare da sayen kwafi dari biyar kan kudi naira dubu dari daya, sai takwaransa na Real Madrid Alhaji Abdullahi Jarumi, ya sayi kwafi dari kan kudi naira dubu ashirin, Shi ma Alhji Yusuf Dankaka kasancewarsa mai goyon bayan kungiyar Real Madrid ya sayi kwafi dari biyu kan kudi naira dubu arba’in.

A nasa jawabin marubucin jaridar Wafiya Wasilu Kawo, ya nuna farin cikinsa tare da godewa mutanen da su ka halarci taron, tare da addu’ar komawa gida lafiya.

 

 

COMMENTS

WORDPRESS: 0
error: Alert: Content is protected !!