HomeFeaturedSIYASA

Ciyaman din Bichi mai barin gado ya yi wani abin mamaki

Shugaban hukumar Bichi mai barin gado Hon. Sani Mukaddas barden sarkin Bichi, ya yi wasu kalamai na ban mamaki, domin a dai-dai lokacin da wa'adin mai

An tsayar da farfesa kuma likita a matsayin Ciyaman a Kano
Kawu Sumaila ya nemi a hukunta Adam Oshieomole
Dan majalisar tarayya Eng Abubakar zai dauki nauyin karatun daliban kimiyya 100 har zuwa jami’a

Shugaban hukumar Bichi mai barin gado Hon. Sani Mukaddas barden sarkin Bichi, ya yi wasu kalamai na ban mamaki, domin a dai-dai lokacin da wa’adin mai mulki ya kare daga wata kujera ya na kokarin neman wani matsayi domin cike gurbi, hakan tasa mutane da yawa a karamar hukumar Bichi, su ke bayyana cewa watakila barde, zai iya neman matsayin majalisar jaha ko tarayya saboda su ne matsayi  da su ka rage masa.

Sai dai ya zuwa yanzu shugaban karamar hukumar, ya kawo karshen wancan tunani, in da ya ce tuni yan uku kansu  a hade ya ke, ba wata kujera da zai nema ko jaha ko tarayya, a barwa Lawan da Abba jagora. Barde ya yi wannan jawabin ne a ofishinsa yau Talata  yayin gabatar da wata ganawa da Bichi Radiyo da Tv

” Magana ake ta ‘yan uku, bayan na kammala mulkin na, kamar yadda wa su ke tunanin zan nemi wani matsayi na kujerar majalisar tarayya ko jaha to a sani babu wuri, Lawan da Abba su ne abin bi”

Hon Barde, a karshe ya kara da godiya ga mutanen Bichi, saboda hadin kan da su ke ba shi wajen sauke nauyi.

 

COMMENTS

WORDPRESS: 1
error: Alert: Content is protected !!