Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bichi kuma shugaban kwamitin ayyuka na majalisar tarayya Eng Abubakar Kabiru Abubakar, ya dauki na
Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bichi kuma shugaban kwamitin ayyuka na majalisar tarayya Eng Abubakar Kabiru Abubakar, ya dauki nauyin matasa hamsin a fadin karamar hukumar Bichi samun hanyoyin dogaro da kai, da ya kunshi karatun kwamfuta da aikin jarida na zamani, sai kuma gyaran setlayit.
Mai temakawa dan majalisar Zaharadden Bello, ya sanar da cewa horon zai gudana karkashin cibiyar BICHI CENTRE FOR JOURNALISM AND MEDIA CREATIV EVENTURES, har tsawon wata uku.
Yanzu haka dai tuni mai temakawa dan majalisar ya sanar da cewa sun fara nazarin zakulo matasan tare da ganin kowanne ya zabi karatun da ya ke muradi.
shi ma cikin wani sakon karfafa gwiwa ga matasan, dan majalisa Eng Abubakar Kabir, ya ce kofarsa a bude ta ke na inganta rayuwar matasan da samar mu su da ayyukan yi
COMMENTS