Dan majalisar tarayya Eng Abubakar zai dauki nauyin karatun daliban kimiyya 100 har zuwa jami’a

HomeFeaturedIlimi

Dan majalisar tarayya Eng Abubakar zai dauki nauyin karatun daliban kimiyya 100 har zuwa jami’a

Daga Zahraddeen Abdullahi Bichi Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bichi kuma shugaban kwamitin ayyuka na majalisar tarayyar kasa Eng

An tsayar da farfesa kuma likita a matsayin Ciyaman a Kano
Za a bude gidan Rediyo da Tv irin su na farko a Kano
Wani Dan majalisar tarayya ya dauki mutane dari da sittin domin su ringa yi Masa shara

Daga Zahraddeen Abdullahi Bichi

Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bichi kuma shugaban kwamitin ayyuka na majalisar tarayyar kasa Eng Abubakar Kabiru Abubakar, ya yi alkawarin daukar nauyin dalibai yan sakandire masu karatun kimiyya daga fadin sassan karamar hukumar, yunkurin hakan ya biyo bayan kudurin dan majalisar na kyankyashe likitoci da injiniyoyi  a nan gaba.
Mai temakawa dan majalisar a kan yada labaran zamani Jamilu Master, shi ne ya shedawa Bichi Radiyo kudurin dan majalisar, a yayin taron mika katin jarabawar shiga makarantun kimiyya ga daliban da aka zabo daga karamar hukumar a makarantun sakandire, in da ya ce duk wanda ya samu nasara dan majalisar ya sha alwashin biya masa kudin makaranta tun daga matakin sakandire zuwa jami’a.
Idan za a iya tunawa a bara, dan majalisar Eng Abubakar Kabiru, ya dauki nauyin yara sama da guda saba’in don yin karatun kimiyya kyauta har su kammala.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
error: Alert: Content is protected !!