Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar birnin Kano, kuma shugaban kwamitin tsaro da bayanan sirri na majalisar tarayya, ya musunta zargin
Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar birnin Kano, kuma shugaban kwamitin tsaro da bayanan sirri na majalisar tarayya, ya musunta zargin da wasu ke yadawa na cewa shugaban hukumar Karota Dr. Baffa Babba, ya ci kwalar rigarsa a lokacin gudanar da zaben raba gardama, na dantakar ciyaman a karamar hukumar birni.
Dan majalisar, ya ce ya yi mamakin jin wannan labari, wanda ya bayyana a matsayin al’mara kuma tatsuniyar gizo da koki, saboda haka ya yi kira da mutane su dunga yin bincike kafin yada labari.
Matemakin dan majalisar ta fuskar yada labarai Faruk Malami Sharada, shi ne ya bayyana haka ga wakilin Bichi Radio da Tv, a yayin wata ganawa ta musamman a yau Talata a birnin Kano, in da ya kara da cewa matsayin Hon Sha’aaban dan majalisa kuma jagoran kwamitin tsaro da bayanan sirri na majalisar, ba wani farar hula da ya ke da karfin ikon rabarsa.
COMMENTS
Allah yakara sutura agareka my hon shaaban Ibrahim sharada never