ENG ABUBAKAR KABIR YA KAWO KARSHEN MATSALAR WUTA A GARIN DAN GAWO

HomeSIYASA

ENG ABUBAKAR KABIR YA KAWO KARSHEN MATSALAR WUTA A GARIN DAN GAWO

Daga Abubakar Haruna Galadanchi Al`ummar garin dan gawo dake karamar hukumar Bichi sun mika godiyar su ga dan majalisar tarayyar yankin Engr

Ciyaman din Bichi mai barin gado ya yi wani abin mamaki

Daga

Abubakar Haruna Galadanchi

Al`ummar garin dan gawo dake karamar hukumar Bichi sun mika godiyar su ga dan majalisar tarayyar yankin Engr Abubakar Kabir Abubakar, saboda magance musu matsalar wutar lantarki da suka shekara tara suna fama sanadiyyar rashin Transfoma.

Jagoran al`ummar garin mallam Hassan, shine yayi wannan yabo yayin mika sabuwar transfoma da dan majalisar ya kai musu, abinda yace sun dade suna hakilon nema shekara da shekaru, sai a wannan lokaci .

“Hakika ya zama wajibi mu godewa dan majalisar mu Gwamnan gobe Eng Abubakar Kabir, saboda kokarinsa na fitar damu daga kangin rashin wuta, abinda mun fidda rai ashe har yanzu akwai masu kishin kasa”

A cikin jawabinsa mai taimakawa dan majalisar ta fuskar yada labaran zamani Jamilu master, ya yi kira ga mutanen garin Dan gawo su ci gaba da yiwa dan majalisar addu`a da shawarwari domin inganta karamar hukumar Bichi.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
error: Alert: Content is protected !!