Ganduje ya sha kasa a jihar Edo

HomeDandalin Siyasa

Ganduje ya sha kasa a jihar Edo

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda ke matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Edo  Fasto Ize Iyamu,  karkashin in

An tsayar da farfesa kuma likita a matsayin Ciyaman a Kano
Kawu Sumaila ya nemi a hukunta Adam Oshieomole

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda ke matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Edo  Fasto Ize Iyamu,  karkashin inuwar jam’iyar APC ya sha kasa . Inda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana sunan Godwin Obaseki, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Hukumar INEC ta bayyana cewa Mista Obaseki, ya samu kuri’u 307,955 yayin da Mista Osagie Ize Iyamu, ya samu kuri’u 223,617.

Ga duk wanda yake biye da sha”anin siyasar jihar Edo, musamman a baya  bayananan, ya kwana da sanin yadda jiga jigan jam”iyar APC wadanda a iya cewa mafi yawancin su na rike da madafun iko, sun yi dafifi a yunkurin hada hannu guri guda  a wani yanayi mai kama da taron dangi, don ganin  dan takarar gwamanan na jam”iyar APC ya samu nasara.

Tun a yammacin yau Asabar, gabanin sanar da sakamakon zaben,  al”ummar kasar nan su ka fara bayyana ra”ayoyin su dangane da yadda zaben ke gudana, har zuwa lokacin da hukumar zabe ta sanar da sunan Mista Godwin Obaseki, a matsayin wanda ya lashe  zaben.

A jihar kano magoya bayan darikar siyasa ta kwankwasiyya, sun bayyana cewa wannan shi ne abin da su ka zaci faruwarsa, tare da kiran abin a matsayin ramuar gayyar abin da ya faru a a Gama a zaben da aka gudanar.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
error: Alert: Content is protected !!