Tsohon mashawarcin shugaban kasa Muhammadu Buhari a majalisar tarayyar kasa Hon. Kawu Sumaila, ya shawarci kunshin shugabancin jamiyar APC na riko
Tsohon mashawarcin shugaban kasa Muhammadu Buhari a majalisar tarayyar kasa Hon. Kawu Sumaila, ya shawarci kunshin shugabancin jamiyar APC na riko a matakin kasa, su gaggauta daukar mataki ga tsohon shugaban jam’iyar Adams Oshiomole da sauran mutanen da ke da hannu saboda faduwar jam’iyar a zaben gwaman jihar Edo da aka gudanar.
Tsohon mashawarcin, Ya yi wannan jawabi yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Kano. Inda ya ce jam’iyar APC an tsara ta kan gudanar da zaben gaskiya, amma saboda da wata biyan bukata ta kashin kai su ka yi watsi da manufar jam’iyar abin da ya janyo tafka asara.
COMMENTS