KOTU TA BADA UMARNIN A KAMO MAWAKI RARARA

HomeLabaran Duniya

KOTU TA BADA UMARNIN A KAMO MAWAKI RARARA

  Daga Abubakar Haruna Galadanchi Babar kotun shariar muslunci dake zamanta a kofar kudu dake birnin kano, karkashin jagorancin mai

Why elementary schools are killing you
Will analysis essays ever rule the world?
11 things that won’t happen in royal societies

 

Daga

Abubakar Haruna Galadanchi

Babar kotun shariar muslunci dake zamanta a kofar kudu dake birnin kano, karkashin jagorancin mai shariah Ibrahim sarki Yola, ta bada umarnin a kamo mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara bisa zargin saka wata matar Aure a cikin wata wakar siyasa mai taken Jihata Jihata ce, lamarin da mijin matar ya bayyana  amatsayin anci mutunci sa.

Tun da fari dai mijin matar mai suna Abdulkadir Inuwa ya gabatar da kokensa ga wata kungiyar kare hakkin dan`adam dake nan kano Global community for Human Right Network domin su taimaka su kwato masa hakkinsa a wajan amwakin dauda kahutu rarara.

lauyan kungiyar ya bayyanawa kotu cewa sun kawo karar ne, bisa bijirewa kiran da suka yiwa mawaki rarara tun a matakin farko, don neman ba`asi da kare kansa amma yayi watsi da bukatar su.

Alkalin kotun mallam Ibrahim sarki yola daga bisani bayan dogon nazari da mai shari`ah Mallam Ibrahim Sarki Yola yayi gami da sashe na 104 sakin layi na hudu cikin baka mai shari’ah, ya bada umarn da a maida wannan kara caji ofishin yansanda dake kwalli domin baturen yansandan wajan wato DPO ya gayyaci dauda kahutu rarara, maryam muhammad da kuma abubakar bashir mai shadda domin ya gudanar da bincike akan lamarin yazo da kansa ba sako ba, kuma babu maganar wakilci, kmaar yadda wakilin Bichi Radio  daya halarci zaman kotun ya rawaito mana.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
error: Alert: Content is protected !!