Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bichi a Arewacin Najeriya Hon Abubakar Kabiru Abubakar, wanda ke matsayin shugaban kwamitin ayyuka
Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bichi a Arewacin Najeriya Hon Abubakar Kabiru Abubakar, wanda ke matsayin shugaban kwamitin ayyuka na majalisar tarayya, ya dauki nauyin mutane dari da sittin aikin shara da tsaftar muhalli a karamar hukumar.
Mai temakawa Dan majalisar kan harkokin kafafan watsa labaran zamani Jamilu Master, Shi ne ya shedawa wakilin Bichi radio da tv cewa, tuni aka ba su horon sanin makamar aiki, inda ya ce Dan majalisar ya yi hakan ne domin Samar da tsaftar garin Bichi a wani take mai suna keep Bichi clean.
Jamilu Master ya kara da cewa, Dan majalisar ya tanaji motar kwasar shara da kayan aiki, yayin da kowanne wata za a ringa biyan su albashin dubu goma kowanne, da nufin bunkasa kiwon lafiyar yankin da Samar da aikin yi.
Cikin wata sanarwa da ya aikewa manema labarai ciki har da Bichi radio, Jamilu Master ya ce, ranar lahadi Dan majalisar tarayya Eng. Abubakar, zai jagoranci kaddamar da dakarun tsaftar muhallin, kazalika sanarwa ta bukaci mutanen da su ka samu aikin bin dokoki da aiki tukuru domin cimma manufar shirin.
COMMENTS