Wani Dan kishin kasa a nan jihar Kano daga yankin karamar hukumar birni, zai bude gidan Rediyo da TV masu zaman kansu, mai suna Hikima, Radio da Hikim
Wani Dan kishin kasa a nan jihar Kano daga yankin karamar hukumar birni, zai bude gidan Rediyo da TV masu zaman kansu, mai suna Hikima, Radio da Hikima Tv na farko a Lardin Afrika.
Jagoran tashoshin wanda ya ke tsohon danjarida ne Suleman Gama, shi ne ya shedawa wakilin BRTV wannan jawabi a jiya asabar, Jim kadan da fitowa daga wani taro a gidan Rediyon da TV.
Cikin jawabin nasa Suleman Gama, ya ce an tanaji kayan aiki na zamani, haka kuma an yi tanajin gogaggun ‘yan jaridu masu kwarewa, inda ya bayyana sunan Usaman Usman, da Zulyadaini Sidi Mustafa Karaye, da Yakubu Musa Fagge, Zakari Yusuf, da sauransu, ya cigaba da cewa nan da Yan kwanaki kadan, tagwayen tashoshin Hikima Radio da Hikima Tv da ke rukunin gidajen Nasarawa G.R.A a layin Titin Jigawa za su Fara gudanar da ayyukansu.
COMMENTS